Ministan kasuwanci na wucin gadi na tsibirin Madagascar ya bada umurnin fitar da shinkafa tan 70 cikin wannan shekara, a wani bayanin da ya fito daga ofishin ministan kasuwancin kasar a ranar Talata. Kudurin ma'aikatar ya baiwa kungiyar manoman "Koloharena Ivolomiarina" dake cikin yankin Amparafaravola a arewa maso gabashin babban tsibirin, daya daga cikin manyan yankunan noman shinkafa, damar da ta fitar da tan 20 na shinkafar da ake kira "shinkafar Dista ko Rojomena" zuwa kasar Amurka. Haka kuma kudurin ya amince da kamfanin Sigma dake Antananarivo, babban birnin kasar, ya fitar da tan 50 na shinkafar Bio zuwa kasar Faransa.
An nuna cewa a cikin yawan nau'o'in shinkafar da ake nomawa a Madagascar, nau'in shinkafar "Rojomena" ya kasance shinkafa mai dadin dandano, dake da suga da kuma girma wadda tuni ta shiga kasuwannin shinkafar Bio na kasashen waje da farashinsu ya kai kashi 30 zuwa 40 cikin 100 da fiye da na shinkafar da aka sani.
Haka dokar amincewar ta zo cikin lokaci, ganin cewa gwamnatin Madagascar ta dauki matakin dakatar da fitar da shinkafa tun a cikin watan Mayun shekarar 2008 dalilan matsalar karancin abinci a duniya. (Maman Ada)