in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara zaben shugaban kasa a kasar Madagascar
2013-10-25 20:47:09 cri
A ranar Jumma'a ne masu kada kuri'a a Antananarivo, babban birnin kasar Madagascar, suka fito kwansu da kwarkwata don zabar sabon shugaban kasar cikin 'yan takara 33 da ke neman wannan mukami.

Duk wanda ya lashe zaben, zai jagoranci kasar na tsawon wa'adin shekaru 5, inda ake saran zai fitar da kasar daga rikicin siyasar da ta tsunduma.

Masu zabe miliyan 7 da dubu 823 da 305  da aka yiwa rijista ne ake saran za su kada kuri'unsu a rumfunan zabe 20,001 da ke sassan kasar.

Bayanai na nuna cewa, runfunan zaben za su kasance a bude har zuwa karfe 5 na yamma agogon wurin kana za a fara kidayar kuri'u nan da nan tare da taimakon kimanin masu sa-ido na kasa da kasa guda 800 da na cikin gida 5000.

Za kuma a yi amfani da jirage masu saukar ungulu guda 10 wajen tattara sakamakon zabe daga rumfunan zabe 186 da ke wurare masu wuyar shiga na kasar.

Ana saran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar(CENIT) za ta bayyana sakamakon wucin gadi cikin kwanaki 10 da kammala zabe, yayin da kotun zabe ta musamman za ta bayyana sakamakon karshe na zaben.

Kamar yadda dokar zaben kasar ta tanada, idan har babu dan takarar da ya samu kashi 50 cikin 100 a zagayen farko na zaben, za a gudanar da zagaye na biyu a ranar 20 ga watan Disamba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China