Daliban na jami'ar kimiyya da fasaha na Antananarivo suna zanga-zangar ne don neman a biya su kudin karo ilimi na watanni ukku da suke bin bashi da saura alawus alawus, kamar yadda daya daga cikin shugabannin daliban Baharo Paul Albert ya yi bayani.
Albert ya ce, bukatunsu ba su da alaka da siyasa, kawai dai suna fama da yunwa ne.
Shi kuma a nasa bayanin, Rakotomahaninna Florens, jagoran rundunar sojin ya ce, daliban suna jifan su da duwatsu ne don haka dole suka maida martini da hayaki mai sa hawaye domin shawo kan yanayin da ake ciki.
Yawancin daliban dake zanga-zangar na jami'o'in al'umma a Madagascar suna zanga-zangar ne game da kudin karo ilimi da a kan ba su.(Fatimah)