in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan kasar Sin dake Nijeriya ya yi ban kwana da mataimakin shugaban kasar
2014-01-08 20:48:23 cri

Jakadan kasar Sin dake Nijeriya Deng Boqing ya yi ban kwana da mataimakin shugaban kasar Namadi Sambo a ran talata 7 ga wata.

A yayin ganawarsu Mr Deng ya isar da gaisuwar fatan alheri daga mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao zuwa ga Alhaji Namadi Sambo.

Jakada Deng san nan ya yi ban kwana ga Namadi Sambo sakamakon kammala wa'adin aikin sa na Jakadar Kasar Sin da ya yi shekaru uku a Nigeria, yana mai nuna godiya bisa ga goyon baya da aka nuna masa da ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya.

A nasa bangare shi kuma, mataimakin kasar na Nijeriya Namadi Sambo shi ma ya mika gaisuwar sa da kyakkyawar fata ga takwaransa na kasar Sin Li Yuanchao ta bakin Mr Deng, yana mai cewa, Nijeriya tana dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Alhaji Nmadi Sambo ya kuma yi fatan zurfafa mu'ammala da hadin kai tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China