in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin CCECC na kasar Sin ya yi bikin fara shimfida hanyar jiragen kasa ta zamani a kasar Nijeriya
2013-04-04 16:05:51 cri
Kamfanin harkokin gine-gine na kasar Sin wato CCECC ya yi biki a ran 3 ga wata a yankin Idu na birnin Abuja hedkwatar kasar Nijeriya da kafa wani babban ginshiki mai kama da harafin Turanci na "T" kuma mai tsawon mita 32, don shimfida hanyar jiragen kasa ta zamani da za ta hada biranen Abuja da Kaduna.

A ran nan da tsakar rana, sakataren ma'aikatar zirga-zirga ta kasar Nijeriya da kuma mataimakin manajan kamfanin CCECC mai kula da harkokin Nijeriya Li Qingyong da dai sauran jami'an kamfanin sun halarci wannan biki kuma sun yanke jan kirtanin da aka gitta.

A gun bikin, Li Qingyong ya nuna cewa, kamfanin ya turo da wata tawagar kwararru tare da kayayyakin aiki na zamani kuma masu inganci domin tabbatar da wannan aikin yadda ya kamata.

Aikin ya kasance mataki na farko wajen shimfida hanyar jiragen kasa ta zamani a kasar Nijeriya da aka fara tun daga ran 19 ga watan Fabrairu na shekarar 2011. Hanyar mai tazarar kilomita 186.5 da zata hade da Abuja da Kaduna zata lakume dalar Amurka miliyan 850, kuma za'a kwashe tsawon watanni 36 ana wannan aiki. Hakazalika hanyar za ta hadawa da tashoshi 9 da gadoji 32, da kuma sauran gadoji 29 masu ratsa hanyoyin mota, da kofofi fiye da 220 inda ruwa za su bi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China