in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata ci gajiyar yarjeniyoyin data sanya hunnu kansu tare da kasar Sin in ji wani masanin tattalin arziki
2013-07-19 14:19:11 cri
Tarayyar Najeriya zata ci gajiyar yarjeniyoyin da ta sanya ma hannu kansu tare da kasar Sin, in ji wani masanin tattalin arziki dake Abuja a ranar Alhamis.

Babban darektan kwamitin kamfanin Boaz na harkokin kasuwanci da kudi, Oluwole Ibikunle ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sa hannu kan yarjeniyoyi a tsakanin kasashen biyu, wani zabi ne mai muhimmanci dake bisa hanya mai kyau.

Mista Ibikunle ya bayyana cewa, shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyarar aiki a ranar 8 ga watan Juli a Birnin Beijing na kasar Sin a karkashin wata babbar tawagar gwamnatin kasar domin sanya hannu kan tarin muhimman yarjeniyoyi tare da kasar Sin. Yarjeniyoyin da aka cimma sun shafi musamman ma yarjejeniyar dangantakar kudi domin tallafawa cigaban tattalin arzikin Najeriya, har ma da yarjejeniyar samun bashi kan shirin fadada filayen saukar jiragen sama hudu na kasar. Haka kuma kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin tattalin arziki da fasaha, da soke kudin takardar visa ga masu fasfo din diplomasiyya ko manyan jami'ai tare da wata yarjejeniyar rigakafin sata, shige da ficen kayayyakin da ba bisa doka ba dasu shafi satar fasaha. Gaskiya wata babbar riba ce ga kasar Najeriya ta fadada hanyoyin makomarta zuwa kasashen waje.

Mista Ibikunle ya kara da cewa tattalin arzikin kasar Sin na samun karuwa cikin sauri, ke nan kasar Najeriya za ta iya samun gajiyar wannan nasara ta kasar Sin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China