in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu kafofin yada labaru a Nijeriya sun yi tunani ga kalaman shugaban babban bankin kasar
2013-04-08 15:12:41 cri

Kwanan baya, shugaban babban bankin Nijeriya Lamido Sanusi ya taba bayyana cewa, Sin na kokarin gudanar da "mulkin mallaka da zalunci" a nahiyar Afrika, a ganinsa, ya kamata nahiyar Afirka ta daidaita matsayin da ta dauka kan kasar Sin.

Game da wannan batu, jaridar "Thisday" ta kasar Nijeriya, ta ba da wani sharhi a ran 7 ga wata, domin bayyana nata ra'ayi ga tsokacin na Lamido Sanusi, inda ta ce wannan hasashe nasa, zai iya kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, musamman ma a fannin tattalin arziki.

Sharhin ya ce, Sin ta musanta abin da Lamido Sanusi ya fadi, kuma mai yiwuwa wannan batu zai shuka barna ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

A cewar sharhin, ya kamata a sake tunani kan irin wannan ra'ayin da aka bayar na nuna barazana ga kasar Sin, tare da waiwayar manufar ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a Afirka kwanakin da suka gabata, shugabannin kasashe da yawa na Afirka suna gani cewa, ikirarin da ake yin a wai kasar Sin take tafiyar da "sabon tsarin mulkin mallaka", zance ne maras tushe, balle makama, haka nan wancan tsokaci na gwamnan babban bankin ya fusata jama'a.

Ban da haka, jaridar ta nuna cewa, yayin ganawar Xi Jinping a nahiyar Afrika, shugaba Xi ya jaddada cewa, halin da duniya ke ciki na canjawa sosai, ana fuskantar zarafi da kuma kalubaloli tare wajen dangakar dake tsakanin Sin da Afirka. Abin da aka tabbatar shi ne, dangantakar sada zumunci tsakanin Sin da Afrika, babban harsashe ne ga tsarin diplomasiyyar Sin. Sa'an nan Sin sahihiyar abokiya ce ga kasashen Afrika har abada, tana kuma ba da taimako daidai gwargwadon karfinta ga bunkasuwar kasashen Afrika cikin lumana. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China