Ministan ma'aikatar harkokin al'adu da yawon shakatawa ta kasar Nijeriya Edem Duke da tawagar 'yan wasan kwaikwayo sama da dari daya dake karkashin jagorancinsa sun halarci bikin bude aikin, inda ya bayyana cewa, kasar Nijeriya tana da dogon tarihi da kyawawan al'adu, don haka yana fatan jama'ar kasar Sin za su kara sanin kasar Nijeriya ta wannan aiki. Haka kuma minista ya yi bayanin cewa, kasar Nijeriya tana son yin cudanyar al'adu a tsakaninta da kasar Sin don sa jama'ar kasar Nijeriya su kara fahimtar al'adun kasashen Asiya ciki har da kasar Sin, da kuma sa kaimi ga hadin gwiwa a fannoni daban daban.
A gun bikin bude aikin, 'yan fasaha daga kasar Nijeriya sun yi rawar da wasan kwaikwayo irin na nahiyar Afirka. (Zainab)