in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kirawo Jakadar kasar Japan a kasarta game da zargin da ake mata na shata yankin tsaronta na sararin samaniya
2013-11-25 20:19:12 cri
A ranar Litinin din 25 ga wata, kasar Sin ta kirawo Jakadan kasar Japan a kasarta domin mai da martani game da korafin da Japan ke yi na shata yankin tsaron sararin samaniya da Sin din ta yi.

Mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen Sin Zheng Zeguang wanda shi ne ya ba da sammaci ga Jakadan kasar Japan din Kitera Masato, ya bayyana dalilin da kasar Sin take da shi na shata yankin tsaron sararin samaniyarta, wanda Japan ta yi korafi a kai a ranar Asabar din da ta wuce, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana cikin wata sanarwa.

Gwamnatin kasar Sin ta ce, shata yankin tsaronta a sararin samaniya a tekun gabas na kasar, wani 'yanci ne da kasar take da shi na kare sararin samaniyarta da yankunanta na doron kasa da kuma kiyaye zirga-zirgar jiragen sama a yankin mallakinta, in ji Mr. Zheng wanda ya jaddada cewar, hakan da ta yi bai keta dokar kasa da kasa ba. Kasashe fiye da 20 da suka hada da Japan duk sun shata yankin sararin samaniyarsu tun daga shekara ta 1950.

Bai kamata ba kasar Japan ta yi kalamai da ba su dace ba a kan abin da Sin ta yi, in ji Mr Zheng. Ya kuma bukaci Japan da ta yi saurin gyara kuskurenta tare kuma da daina yin ayyukan da za su kawo sabani a tsakanin yankuna sannan ta guji yin abin da zai lalata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China