in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen Sin, Jamus, Indonesiya, Afrika ta kudu da Vietnam
2013-09-27 16:58:11 cri

A ran 26 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Jamus Guido Westerwelle, da na kasar Indonesiya Marty Natalegawa, da na Afrika ta kudu Maite Nkoana-Mashabane da na kasar Vietnam Phim Binh Minh a birnin New York hedkwatar MDD, kuma ya halarci taron ministocin harkokin waje na kasashe mambobin kungiyar BRICS.

Yayin ganawar, Mr Wang Yi ya bayyana cewa, Sin ta dora babban muhimmanci kan ragowar ayyukan tabbatar da shirin aikatawa na Durban. Game da batun kasar Sham, Wang Yi ya jaddada wajibcin kara tuntubar juna tsakanin mambobin kasashen BRICS, domin nacewa ga hanyar warware rikicin kasar Sham a siyasance da kiyaye tsarin mulkin MDD.

Bugu da kari, Wang Yi ya furta cewa, an samu ci gaba a fannin kafa bankin samun bunkasuwa da asusun ko ta kwana yayin kwarya-kwaryar ganawar shugabannin kasashen BRICS a birnin Saint-Petesburg. Ya kamata, kasashen biyar su kafa wadannan mayan tsare-tsare biyu da sauri tare kuma da kafa tsarin hada-hadar kudi domin tinkarar sauyin yanayi a fannin kasuwar duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China