in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya buga waya ga bangarorin da abin ya shafa kan batun Syria
2013-08-30 15:33:19 cri
A ranar Alhamis 29 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya buga waya ga babban sakataren MDD, Ban Ki-moon, da ministan harkokin waje na Jamus Guido Westerwelle, da kuma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Nabil Al'araby kan yanayin da ake ciki a Syria.

Yayin da yake magana da Ban Ki-moon, Wang Yi ya jaddada cewa, Sin a tsaye take tsayin daka na goyon baya kan rukunin masu yin bincike wajen gudanar da aikinsu ba tare da fuskantar wani shinge ba kuma cikin adalci. Don haka kamata ya yi bangarori daban daban su samar da yanayi mai kyau kan wannan batu don haka bai kamata a matsa ma kwamitin sulhu na MDD lamba ba wajen daukar matakai kafin a kammala yin binciken, a cewar sa babu hanyar da zai kawo daidaito a batun Syria sai ta siyasa kawai.

A nasa bangaren Ban Ki-moon ya nuna yabo kan ra'ayin kasar Sin wadda take sauke nauyinta a koda yaushe, kuma ya amince da cewa kamata ya yi a daidaita batun Syria ta hanyar siyasa, yana mai fatan kara yin mu'amala da Sin game da batun na Syria.

Yayin da ya buga waya ga takwaransa na Jamus da kuma babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, Wang Yi ya jaddada cewa, Sin ba ta amince da duk wanda zai yi amfanin da makamai masu guba ba. Rukunin yin bincike na MDD yana aiki a Syria domin gano ko an yi amfani da makamai masu guba da kuma su wa suka yi amfani da su, domin hakan zai taimaka wajen daidaita batun yadda ya kamata, kuma kamata ya yi a dauki alhaki kan tarihi a wannan fanni.

Ban da haka, Wang ya nanata cewa, kamata ya yi bangarori daban daban su yi hakuri kan batun yaki da kuma zaman lafiya, kowanen su ba zai iya daidaita matsala ba ta hanyar daukar matakai da kansa, ganin hakan ba ya bisa doka.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China