Wang Yi ya ce, gwamnatin Sin za ta ci gaba da mayar da batun samun ci gaba cikin dogon lokaci a matsayin wata babbar manufa ta kasar, tare da jaddada cewa, kasar Sin ba za ta bi hanyar gurbata yanayi a farko, sannan ta yaki da shi ba, ya kamata ta dauki alhakin da ke wuyanta.
Wang Yi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su kara karfi wajen kiyaye muhallin halittu don cimma burin samun bunkasuwa cikin dogon lokaci, kuma Sin za ta nace ga bin ka'idar "daukar nauyi iri daya yayin da ake amincewa da bambancinsa", don kirkiro da sabbin manufofi, kuma za ta mai da hankali game da raya ingancin kayayyaki. Yayin da kasar Sin take karfafa aikin raya tattalin arziki don samun ci gaba cikin dogon lokaci, za ta mayar da aikin kyautata zaman rayuwar al'umma da samar da daidaito a zamantakewar al'umma a gaban kome.(Bako)