in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Sudan
2013-08-23 16:00:27 cri

A ran 22 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Sudan Ali Ahmed Karti, wanda ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing.

Yayin ganawar tasu, Wang Yi ya nuna cewa, Sin na daukar kasar Sudan a matsayin kawa ta musamman, kuma tana fatan kara hadin gwiwa da Sudan din, ta yadda za su inganta aminci ta fuskar diplomasiyya, da habaka hadin gwiwa a fannin ciniki da tattalin arziki, tare da ingiza dangantakar hadin kai ta sada zumunci tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi.

A nasa bangare, Ali Ahmed Karti ya jinjinawa ci gaba mai kyau da bangarorin biyu suka samu, wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, tare da godiya ga taimako mai daraja da Sin ke baiwa kasarsa, yana mai cewa, kasar Sudan na fatan kara hadin gwiwa da Sin, wajen raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi a nan gaba.

Dadin dadawa, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta kudu. Don gane da hakan, Wang Yi ya ba da wasu shawarwari da za su taimaka, wajen warware rikicin dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin shawara. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China