in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta taimaka wa yankin Asiya da tekun Pasific wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa
2013-07-02 21:00:56 cri
A ranar 2 ga wata a birnin Seri Begawa dake kasar Brunei, ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya halarci taron ministocin harkokin waje na yankin kungiyar ASEAN, inda ya nuna cewa, neman samun zaman lafiya ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa, samun bunkasuwa tare ta hanyar bunkasa tattalin arziki bisa tsarin bai daya, yin hadin gwiwa da kuma daidaita matsaloli su ne hanyar da za a yi amfani da ita kawai wajen cimma burin samun zaman lafiya da wadata mai dorewa a yankin Asiya da tekun Pasific, kana ya kamata bangarori daban daban su dauki nauyin dake wuyansu a wannan fanni. Makomar kasar Sin tana da nasaba da zaman lafiya da bunkasuwar yankin Asiya da tekun Pasific. An nuna cewa, Sin za ta taimaka wa yankin wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa. Burin kasar Sin ya dace da bukatun jama'ar yankin har ma a dukkan duniya wajen samun zaman lafiya da bunkasuwa, cimma wannan burin kasar Sin zai sa kaimi ga Sin da ta kara yin hadin gwiwa da yankin Asiya da tekun Pasific har ma da dukkan duniya, kana Sin za ta kara bayar da damar hadin gwiwa da bunkasuwa ga kasa da kasa. Kasar Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa wajen maida karni na 21 a matsayin karni na samun zaman lafiya da bunkasuwa a yankin Asiya da tekun Pasific, da bada gudummawa wajen kyautata makomar duniya gaba daya. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China