in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin manyan jami'an kasar Sin da na Zimbabwe
2013-09-25 16:57:56 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, a jiya Talata 24 ga wata a hedkwatar MDD dake birnin New York.

Yayin ganawar tasu Wang Yi ya nuna cewa, Sin za ta hada kai da kasashen Afrika, ciki hadda Zimbabwe domin kara ingiza dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, ta yadda jama'ar kasashen za su ci gajiyar dake tattare da hakan.

A nasa bangare shugaba Mugabe ya furta cewa, Zimbabwe ta nace ga matsayin daukar matakin koyi da kyawawan darussa daga gabashin duniya, kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, dake taimakawa nahiyar Afrika a kowane lokaci, baya ga aniyarta ta hada kai da kasashen dake nahiyar, bisa ka'idar mutunta juna, adalci da cimma moriyar juna. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China