Ta bakin kakakinsa, da kakkausan murya Mr. Ban Ki-moon ya yi alla wadai kan harin boma-bomai da aka kai wa wani bankin dake birnin Kidal na kasar Mali, kuma ya yi kira da a hukunta wadanda suka kai wannan farmaki. A sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, MDD za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jama'a da gwamnatin kasar Mali wajen kiyaye zaman lafiyar kasa cikin dogon lokaci kamar yadda ta saba yi. Kuma Mr. Ban Ki-moon ya yi kira ga jama'ar kasar Mali da su nuna adawa da duk wasu aikace-aikacen da za su janyo tashi hankali a kasar, ya kamata su nuna goyon baya ga ayyukan shimfida zaman lafiya a kasa ta hanyar halartar zaben majalisar dokokin kasa zagaye na biyu da za a yi a ran 15 ga wata tare da bin sauran hanyoyin zaman lafiya.
Haka zalika, a ran 14 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa ta kafofin watsa labarai, inda ya kuma yi suka kan farmakin da aka kai wa sojojin kiyaye zaman lafiya da ya tura kasar Mali. Kuma kwamitin ya sake jaddada goyon bayansa ga sojojin da kuma rundunar sojan kasar Faransa dake kasa ta Mali, sa'an nan kuma, ya yi kira ga gwamnatin kasar Mali da ta gudanar da bincike kan lamarin cikin sauri, domin hukunta masu hannu kan farmakin yadda ya kamata. Bugu da kari, kwamitin ya sake nanata cewa, zai ci gaba da ba da goyon baya ga gwamnatin kasar Mali da sojojin kiyaye zaman lafiya dake kasar Mali kan ayyukansu na kiyaye zaman karko a kasar Mali, ta yadda za a farfado da hukumomin kasar da kuma yin shawarwarin siyasa tsakanin bangarorin daban daban yadda ya kamata. (Maryam)