in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Faransa sun kashe 'yan tawaye 19 a arewacin Mali
2013-12-11 10:36:45 cri

Rundunar sojan kasar Faransa ta bayyana cewa, sojojinta da ke aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Timbuktu da ke arewacin kasar Mali, sun halaka 'yan tawaye 19 a ranar Talata.

Sojojin na Faransa da takwararsu ta kungiyar AU da kuma sojojin kasar ta Mali, sun shafe makonni suna aikin kakkabe 'yan tawaye a arewacin kasar da har yanzu kananan kungiyoyin 'yan tawaye irin su kungiyar Al-Qaida reshen arewacin Afirka wato AQIM ke da karfi, duk da cewa, an fattake su a watan Janairu daga garuruwan Gao, Timbuktu da kuma Kidal.

Wadannan sojoji na daukar matakai ne da nufin karfafa matakan tsaro kafin zagaye na biyu na zabukan da za a gudanar a ranar Lahadi, bayan zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 24 ga watan Nuwamba.

Tun a watan Maris din shekarar 2012 ne, kasar ta Mali ta fara farfadowa daga radadin yaki, lokacin da kungiyar AQIM da sauran 'yan tawaye suka mamaye arewacin kasar ta Mali, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Sai dai sojojin kasar sun samu karfin gwiwar komawa arewacin kasar a watan Janairu, bisa goyon bayan dakarun Faransa da na Afirka, lamarin da ya ba da damar gudanar da zaben shugaban kasa cikin nasara a watan Agusta. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China