Bamako, babban birnin kasar Mali ya kasance dandalin manyan abubuwa biyu da suka gudana a ranar Laraba da safe wadanda suka hada da zanga-zangar kin jinin kungiyar neman 'yancin yankin Azawad ta MNLA da kuma cafke janar Amadou Haya Sanogo, jagoran tsoffin sojojin da suka hambarar da shugaba Amadou Toumani Toure a cikin watan Maris din shekarar 2012. Kawancen kungiyoyin kare 'yancin kasar Mali dake Kidal da suke kunshe da kungiyar direbobi da 'yan kasuwa, kungiyar mabiya akidar Rasta na kasar Mali da kungiyar nakasassu, dukkansu a karkashin jagorancin Mohamed Bathily suka gudanar da wannan zanga-zanga. Yin Allawadai da kyaluwar rundunar sojojin kasar a yankin Kidal, da alfarmar da kasar Faransa ke baiwa 'yan tawayen MNLA da kuma yin kira ga tawagar kungiyar MDD ta MINUSMA da ta yi aikinta yadda ya kamata na daga cikin manyan batutuwan da masu zanga-zangar suka tabo, in ji mista Mohamed Bathily, kakakin wannan kawance kuma 'dan ministan shari'ar kasar Mali Mohamed Ali Bathily. Zanga-zangar ta tashi tun daga dandalin 'yancin kasar Mali, da ke nisan mita 300 daga gidan janar Sanogo.
Daga nan zauren taron kasa da kasa (CICB) dake birnin na Bamako bayan gidan janar Sanogo, 'yan jaridar kasar Mali sun tabbatar da cewa, sun ga lokacin da manyan jami'an rundunar sojojin kasar kamar su janar Didie Dakoua, mataimakin shugaban rundunar sojojin kasar a cikin maharabar CICB.
Daga bisani wata majiyar sojojin kasar ta tabbatar da cewa, janar Sanogo ya shiga hannun jami'an tsaro bisa zargin da ake masa na cin amanar kasa. (Maman Ada)