Bayan ganarwarsu, mista Louis Milchel ya bayyana cewa, shugaban kasar Mali ya yi imanin cewa, ya kamata zabubukan 'yan majalisa su gudana yadda ya kamata kuma cikin nasara domin wadannan zabubuka sun kasance wani sharadi na biyu da ya wajaba wajen maido da tsarin demokaradiya tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Mali.
Mista Louis Michel ya nuna cewa, majalisar dokokin kasar Mali ya kamata ta yi aiki domin karfafa aikin gwamnati, kuma shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita na sane da kalubaloli da ayyukan da suka shafi hada kan 'yan kasa, batun arewacin kasar da sauransu.
Idan ba'a manta ba, tawagar sanya ido kan zabe ta kungiyar EU ta je kasar Mali a yayin zabubukan shugaban kasa zagaye na farko da na biyu da suka gabata. Ga wadannan zabubuka na 'yan majalisa, ta sake dawowa da wata tawagar kwararrun dake kunshe da masu sa ido kusan dari da za su sanya ido a tashoshin zabe a dukkan fadin kasar ta Mali. (Maman Ada)