Ofishin kula da harkokin kiyaye zaman lafiya na ma'aikatar tsaron kasar Sin ya bayyana cewa, bayan isowarsu a yankin Gao na Mali, sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin sun fara daidaito kan yanayin tsaro da kuma yanayi mai zafi sosai a can, tare da shirya tantuna da kafa shingayen kariya. Yanzu sun riga sun kammala shiri don karbar duk ayyukan da za a basu.
Baki daya rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta Sin a Mali zagaye na farko ta hada da sojoji 395, wadanda aka kebe su zuwa rukunin sojojin injiniyoyi, da na ba da jiyya, da na yin rangadi. Yanzu sauran sojojin kasar Sin su ma sun kammala shirinsu domin a girke su a Malin, kuma za su iya tashi bisa lokacin da MDD ta sanar.(Fatima)