Gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta fidda wata sanarwa game da shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas
Gwamnatin jamhuriyar jama'ar kasar Sin ta sanar da shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas bisa "dokokin tsaron kasa na jamhuriyar jama'ar kasar Sin" wadanda aka samar a ranar 14 ga watan Maris na shekarar 1997, da "dokokin kula da harkokin sararin samaniya na jama'ar jamhuriyar jama'ar kasar Sin" da aka fitar ran 30 ga watan Oktobar shekarar 1995 da kuma "ka'i'dojin da jiragen sama suke bi na jamhiriyar jama'ar kasar Sin" da aka samar a ranar 27 ga watan Yulin shekarar 2002.
Haka zalika, gwamnatin kasa ta sanar da cikakken bayani game da inda za a shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas suke. (Maryam)