Game da dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta tsai da yankin shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas da kuma ko lamarin na da alaka da yanayin tsaron yankin, Mr. Yang ya bayyana cewa, kasar Sin ta tsai da yankin shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas ne bisa ka'idojin kasa da kasa don kiyaye mulkin kai, tsaron kasa da na sararin samaniya, da kuma kare ka'idojin da ya kamata jiragen sama su bi. Wannan shi ne matakin da ya kamata kasar Sin ta dauka wajen gudanar da ikonta kan kiyaye tsaron kasa.
Yayin da ake tsokaci kan ka'idojin da gwamantin kasa take bi wajen shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas, Mr. Yang ya bayyana cewa, gwamnatin ta gudanar da aikin ne bisa dokokin kasa wadanda suka dace da ka'idojin kasa da kasa.
Yayin da ake tsokaci kan matakan da kasar Sin za ta dauka idan har jiragen sama na kasashen ketare suka kutsa yankin shata sassan tsaron sararin samaniya na Tekun Gabas, Mr. Yang ya ce, kasar Sin za ta dauki matakan gano asali, da sa ido, da yin bincike da dai sauran matakai yadda ya kamata don kiyaye tsaron kasa. Kuma tana fatan bangarorin da abin ya shafa za su yi hadin gwiwa kan aikin tsaron kasa don kiyaye tsaron sararin sama tare. (Maryam)