Manyan jami'an kasar Sin da na Rasha sun shelanta niyyarsu a ranar Alhamis a birnin Moscow wajen karfafa yin aiki tare da bunkasa dangantakar dake tsakaninsu a yayin zagaye ta tara na shawarwari kan dabarun tsaro tsakanin kasar Sin da kasar Rasha.
Mashawarcin kasa na kasar Sin Yang Jiechi da sakataren kwamitin tsaron kasar Rasha Nikolai Patrouchev sun amince cewa, ziyarar shugaban kasar Xi Jinping a kasar Rasha a cikin Maris din da ya gabata ta sanya wani sabon jini kan cigaban dangantaka dake tsakanin kasashen biyu da bayyana sabon hange wajen tabbatar da hulda ta manyan tsare tsare tsakanin kasashen biyu.
Ya kamata kasashen Sin da Rasha su cigaba da karfafa tuntubar juna, aiki tare da hadin gwiwa bisa tushen dangantaka ta gaskiya, girmama yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma domin ingiza cigaban wannan dangantaka, in ji manyan jami'an bangarorin biyu.
Haka zalika, bangarorin biyu sun amince wajen kara bunkasa hanyar yin shawarwari kan dabarun tsaro, ta yadda za'a ba da muhimmanci mafi kyau wajen bunkasa huldodin sada zumunci.
A cikin wannan duniya mai wuyar al'amari da muhimman sauye sauye da ake samu, kasar Sin da kasar Rasha suna bukatar su girmama junansu da kuma amincewa da junansu, taimakawa juna tsakaninsu wajen kare da kiyaye 'yancin kasashensu, tsaro da zaman lafiya da kuma maradunsu na samun cigaba, in ji manyan jami'an bangarorin kasashen biyu.
Haka kuma, wakilan kasashen biyu sun dauki niyyar fadada ayyukansu tare a fannin harkokin kasa da kasa, kiyaye manufofi da ka'idodin kundin MDD da dokokin dangantakar kasa da kasa, ta yadda za'a iyar daidaita duk wasu manyan batutuwa cikin ruwan sanyi domin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban duniya da na shiyya shiyya.
Kasashen Sin da Rasha za su kara kokarinsu cikin hadin gwiwa domin ganin an cimma nasara a babban taron kasashen G20 da za'a shirya a cikin watan Satumba mai zuwa a birnin Saint-Petersbourg na kasar Rasha da kuma babban taron kungiyar hadin gwiwar Shanghai OCS da zai gudana a birnin Bichkek na kasar Kirghizistan. (Maman Ada)