in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan batutuwan da suka shafi Afirka da Gabas ta Tsakiya na kan gaba a ajandar kwamitin tsaron MDD
2013-11-08 10:40:42 cri

An bayyana batutuwan da suka shafi kawo karshen tashe-tashen hankula a nahiyar Afirka, da Gabas ta Tsakiya, a matsayin batutuwan da suka fi mamaye ayyukan kwamitin tsaron MDD tsakankanin watan Agustan bara, zuwa watan Yulin wannan shekara da muke ciki.

Jagoran kwamitin tsaron na karba karba, kuma wakilin din din din na kasar Sin a MDD Liu Jieyi ne ya bayyana hakan ga mahalarta zaman MDD da ya gudana a ranar Alhamis, yayin da yake gabatar da rahoton shekara-shekara na kwamitin tsaron majalissar. Liu ya ce, kimanin kaso 60 bisa dari na ajandar ayyukan kwamitin na tsaro ta shafi batun nahiyar ta Afirka, yayin da rabin tawagogin wanzar da zaman lafiyar majalissar ke wannan nahiya.

Manzon kasar ta Sin ya kara da cewa, bisa hadin gwiwar da kwamitin tsaron ya gudanar da kungiyar AU, da ma ragowar kungiyoyin nahiyar, an kai ga cimma nasarar shiga tsakani, a rikicin siyasar da ya addabi kasashen Mali, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, da kasar Somalia, da Sudan da kuma Sudan ta Kudu. Har ila yau Liu ya ce, kwamitin ya yi iyakacin kokarinsa wajen habaka zaman yanayin lafiya da lumana a yankuna da dama a Gabas ta Tsakiya, ciki hadda tabbatar da ci gaban shawarwari tsakanin mahukuntan Falasdinu da na al'ummar Isra'ila.

Bugu da kari kwamitin ya yi namijin kokari wajen ganin an gudanar da tattaunawa sau da dama tsakanin 'yan adawa, da tsagin mahukuntan kasar Sham. Baya ga bibiyar halin da ake ciki a kasashen Lebanon, da Libya, da Iraq da Yemen da ma ragowar yankunan na Gabas ta Tsakiya.

Don gane da batun tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa kuwa, Mr. Liu ya ce, karkashin kwazon kwamitin tsaron majalissar, an fidda tsare-tsare da dama, wadanda suka taimaka ga hadin gwiwar kasashen duniya, a fagen yaki da ayyukan ta'addanci, da yaduwar kananan makamai, da yawaitar manyan laifukan da suka shafi kasa da kasa,tare da bunkasa hadin kai wajen fuskantar kalubalolin tsaro tsakanin daukacin kasashen duniya. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China