in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun sojan Syria sun sake kwato wasu manyan wurare dake kusa da Damaskus
2013-10-25 10:03:16 cri

A ranar Alhamis din nan 24 ga wata, rahotanni daga kasar Syria sun nuna cewa, dakarun sojan kasar sun samu nasarar kwato wassu manyan wurare dake kusa da Damaskus, abin da ya ba da cikakken ikon rinjayen mallakarsu daga hannun 'yan tawaye a gabashin babban birnin kasar.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar SANA ya ruwaito, sojojin sun kwato yankin Htaitet al-Turkman dake karkarar kudu maso gabashin Damaskus bayan arangama da aka yi ta awoyi 48 tsakaninsu da 'yan tawaye wadda ta yi sanadiyar mutuwar 'yan tawayen akalla 100.

Game da hakan, wassu masana game da ayyukan soji sun bayyana cewa, wannan sabuwar nasara tana da muhimmanci sosai saboda kwacen da aka yi ya tabbatar da cewar, yanzu hanyar zuwa filin saukar jiragen sama na babban birnin ya samu kariya daga harin ababen fashewa da 'yan tawaye ke yi a kan babban birnin.

Yanzu da aka kwato wuraren, 'yan tawayen wadanda suke gabashin garin al-Ghouta, an kewaye su daga kowane bangare, an kuma dakushe musu duk wani karfin aiwatar da wani hari nan gaba.

Wannan sabuwar dabara da dakarun sojan kasar suka aiwatar na karfafa tsaro a duk inda 'yan tawaye suke, kuma ta ingiza 'yan tawayen aiwatar da harin na rokoki daga inda suke zuwa yankunan dake cikin Damaskus, duk da cewar, 'yan tawayen na ikirarin cewa, harin da suke aikawa a kan sansanin sojojin kasar da wuraren tsaro, amma a zahiri harin na afkawa a kan unguwannin da fararen hula suke zama, abin da ya yi sanadiyar asarar rayuka da jikkatar fararen hulan da suka hada da mata da yara. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China