Rahotanni daga tsagin wakilcin al'ummar Falasdinu, dake ci gaba da ganawa da jami'an kasar Isra'ila na bayyana cewa, mahukuntan Isra'ila sun tsaya kai da fata cewa, batutuwan da suka shafi tsaro ne kadai za a tattaunawa a kansu, yayin ganawar baya bayan nan da bagarorin biyu suka shiga.
Wani jami'i daga tsagin al'ummar Falasdinu da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, Isra'ila ta ki yarda ta tattauna ragowar batutuwan da suka shafi shirin warware matsalolin da ke tsakanin bangarorin biyu yayin zaman taron da aka gudanar a birnin Kudus.
Jami'in wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, bayan kammalar zaman taron da sassan biyu suka gudanar a ranar Talata, ya ce, Isra'ila ta gabatar da wasu kudirori da ke da nasaba da kare iyakokinta, ciki hadda batun kafa na'urorin sa ido a yankin yammacin kogin Jordan. Har ila yau an tafka mahawarar mai zafi don gane da bukatar girke jami'an tsaron Isra'ila a kan iyakar dake gabashin yankunan al'ummar Falasdinu, masu iyaka da kasar Jordan, bukatar da tsagin Falasdinun ya yi watsi da ita.
Da yake karin haske kan yanayin da ake ciki a halin yanzu, daya daga jagororin kungiyar PLO ta al'ummar Falasdinu Yasser Abed Rabbo, ya ce, babu wani ci gaba na a zo a gani da aka cimma kawo wannan lokaci. A cewarsa, kwalliya za ta biya kudin sabulu ne kadai, idan har kasar Amurka ta matsa lambar cimma kudurin wanzar da zaman lafiya tsakankanin bangarorin biyu. (Saminu)