Bisa sakon da fadar shugaban kasar ta Amurka ta fitar, an ce, shugaba Obama ya sanar da majalisar dokokin kasar cewa, za a sabunta tsarin tsaron kasa, tare da tabbatar da muhimman batutuwa masu alaka da ba da kariya ga kasar a wa'adin aikinsa na biyu.
A watan Mayun shekarar 2010 ne dai shugaba Obama ya gabatar da rahoton tsaron kasar Amurka bisa manyan tsare-tsare, wanda ya fayyace wasu muhimman batutuwa, kamar tabbatar da matsayin Amurka na yin jagoranci a duniya, da kawo karshen yakin Iraki, da yaki da kungiyar Al-Qaeda da sauransu. Har wa yau, an shigar da farfado da tattalin arzikin kasar cikin wannan rahoto.
Ban da haka ma cikin rahoton na shekarar 2010, an zayyana daukar matakin soja, a matsayin mataki na karshe bayan kokarin diplomasiyya ya faskara, inda aka yi kira ga Amurka da ta kara hadin gwiwa da Sin, da Indiya, da ma sauran manyan kasashen duniya masu karfin fada-a-ji wajen samar da ci gaba. (Fatima)