in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Samun daidaito a fuskar tsaro shi ne zai tabbatar da nasarar shirin mika mulki a Afghanistan
2013-06-21 10:20:59 cri

A ranar Alhamis, wani jakadan kasar Sin ya jadadda muhimmancin samun daidaito kan yanayin tsaro a kasar Afghanistan don a samu nasarar shirin mika mulki, inda kuma ya bukaci bangarori su kare fararen hula.

Mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD, Wang Min shi ne ya bayyana hakan yayin wata ganawar kwamitin sulhu na MDD dangane da batun Afghanistan.

Jakadan na kasar Sin ya lura cewa, samun daidaito a fuskar tsaro na da muhimmanci matuka ga cimma nasarar shirin mika mulki a kasar, don haka ya bukaci dukkan bangarori su ci gaba da kiyaye dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da ma sauran muhimman dokoki na duniya don sauke nauyi dake wuyansu na kare fararen hula.

A halin da ake ciki, jakadan na kasar Sin ya yi kira ga al'ummomin duniya da su cika alkawurransu na ba da tallafi ga Afghanistan don a samu ingancin harkokin bunkasa.

Wang har ila yau ya yi nuni da cewa, cimma nasarar gudanar da zabe a shekarar 2014 a Afghanistan na da muhimmanci ga tabbatar da dorewar kokarin kafa zaman lafiya a kasar, inda kuma ya nuna burin ganin cewa, jama'ar Afghanistan za su ci gaba da amfani da tattaunawa da kuma shawarwari don shawo kan banbance-banbance, da ma tabbatar da nasarar zabe. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China