in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu
2013-12-06 17:52:21 cri

'Yar wasan kwallon golf ta kasar Sin Feng Shanshan ta lashe gasar LPGA ta kasar Amurka.

Daga wasan tsere sai kuma Golf, inda labaran baya bayan nan ke cewa, Feng Shanshan 'yar wasan kwallon golf ta kasar Sin, ta lashe gasar wasan kwallon golf ta LPGA ta kasar Amurka, tare kuma da samun kyautar kudi har dalar Amurka dubu 700, baya ga matsayin ta da ya daga zuwa 4 a duniya.

Wannan ne dai karo na biyu da Feng Shanshan ta zama zakara a gasar ta LPGA, nasarar da ta taba samu ta lashe gasar LPGA ta kasar Sin a watan Oktobar bana.

An haifi Feng Shanshan ne dai a birnin Guangzhou na kasar Sin, ta kuma fara koyon wasan kwallon golf tun ta na da shekaru 10 da haihuwa. Ta kuma fara shiga gasar LPGA tun a shekara ta 2008. A tsakanin wadannan shekaru ta shiga gasanni da dama a kasar Amurka. (Saminu Alhassan/Zainab)


1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China