in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Labarai na dumi-dumi game da gasar cin kofin duniya
2013-10-10 20:34:14 cri


ANA SAMUN KARUWAR MASU BUKATAR SAYEN TIKITIN KALLON GASAR CIN KOFIN DUNIYA TA BRAZIL.

Yayin da aka riga ya aka fara sayar da tikitin kallon wasannin gasar cin kofin duniya ta kasar Brazil dake tafe a shekarar 2014 mai zuwa a matakin farko, yawan bukatar sayen tikitin a kan shafukan yanar gizo a ranar farko ya kai miliyan 2, da dubu dari Uku. Kawo kuma wannan lokaci da ake ci gaba da sayar da tikitin yawan mabukatansa sun kai ga mutum miliyan 4 da dubu dari 5.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, mutanen kasar Brazil sune a kan gaba wajen sayen tikitin gasar, inda yawan bukatar da suka nuna ta neman mallakar tikitin fiye da miliyan 3, kimanin kashi 77 cikin dari ke nan na dukkan bukatar da aka nuna. Bayan su, sai kasar Argentina, wadda ta zama a matsayi na biyu, sannan Amurka dake matsayi na uku. Kuma bisa la'akari da bukatun masu sayen tikitin kallon gasar, ance mutane sun fi nuna sha'awar su, ta kallo wasan farko a gasar, wanda za a yi a ranar 12 ga watan Yuni, da kuma wasan karshe na gasar, da za a yi a ranar 13 ga watan Yulin shekarar ta badi.

FIFA ZA TA YI SHAWARWARI KAN BATUN SAUYA LOKACIN GUDANAR DA GASAR CIN KOFIN DUNIYA TA SHEKARAR 2022.

Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, ta tsaida kudurin gudanar da shawarwari kan batun canja lokacin gudanar da gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Qatar a shekarar 2022.

Shawarwarin da aka shirya gudanarwa a birnin Zurich dake kasar Switzerland a ranar 4 ga wata, sun shafi batun yiwuwar sauya lokacin gasar zuwa lokacin sanyi.

Kwamitin gudanarwar hukumar ta FIFA ya bayyana cewa, za a gudanar da shawarwarin ne tsakanin hukumar FIFA, da hukumomin hadin gwiwa na wasan kwallon kafa na yankuna daban daban, da kungiyoyin wasan kwallon kafa, da 'yan wasa, da kuma kamfanonin hadin gwiwar hukumar. Har ila yau kasancewar sai nan da shekaru 9 masu zuwa ne za a gudanar da gasar cin kofin duniyar ta kasar Qatar, babu wata bukatar tsaida kuduri game da wannan batu cikin sauri. Kwamitin ya kara da cewa, babu bukatar tsaida kudurin kafin gasar cin kofin duniya da za a yi a kasar Brazil a shekara mai zuwa.

Yanayin zafi dai kan tsananta kwarai a lokacin bazara a kasar ta Qatar, dake yankin gabas ta tsakiya. Inda ma'aunin zafi tun daga watan Yuni zuwa Agusta kan kai kimanin degree Celsius 50. Hakan ne ya sanya bayan da kasar ta Qatar ta samu iznin daukar bakuncin gudanar da gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022, aka yi ta samun kiraye-kirayen canza lokacin gudanar da gasar zuwa lokacin sanyi. Sai dai fa ba dukkanin bangarori ne suka amince da hakan ba. An ce, wannan batu da ya shafi gasar cin kofin duniya ya jawo hankalin kasashen duniya matuka. Ga misali idan har aka canja lokacin gudanar da gasar zuwa lokacin sanyi, hakan na iya kawo matsala ga sauran gasannin da ake yi a lokacin na sanyi.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China