in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu
2013-12-06 17:52:21 cri

'Yan tseren kasar Habasha sun lashe gasar gudun yada kanin-wani da ya gabata a birnin Guangzhou.

Daga kasar Italiya bari kuma mu dawo nan kasar Sin, inda a 'yan kwanakin baya ne aka gudanar da gasar gudun yada kanin-wani a birnin Guangzhou na nan kasar Sin, inda 'yan tsere fiye da dubu 20 daga kasashe kimanin 38, ciki hadda Habasha, da Kenya, da Morocco, da Tanzania, da Australia, da Faransa, da Jamus, da Indiya, da Argentina da sauransu suka halarta.

A wannan karo an gudanar da wasanni zahaye 3, da suka hada da gasar gudun yada kanin-wani ta cikakken zango, da ta rabin zango, da kuma gasar gudun kilomita 5. A karshe dai, dan tseren kasar Habasha Sisay Jisa Mekonnen ya zama zakara a gasar gudu ta ajin maza ta cikakken zango, cikin sa'oi 2 da mintuna 11 da dakika 25, yayin da 'yan tseren kasar Kenya suka zama a matsayi na biyu da na uku. A gasar mata ta cikakken zango ma, 'yar tsere daga kasar Habasha Goitetom Haftu Tesema ce ta zama zakara bayan ta kammala gudun ta cikin sa'oi 2 da minti 39 da dakika 17, haka kuma 'yan tsere daga kasar Kenya suka zama a matsayi na biyu da na uku.

Hanyar gudun da 'yan tseren suka bi ta ratsa gabobi biyu na kogin Zhu, wanda hakan ya sanya hukumar lura da harkokin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, ta maida hanyar a matsayin daya daga cikin hanyoyin gudun yada kanin-wani mafiya kyaun gani a duniya.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China