in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu
2013-12-06 17:52:21 cri


Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu.

Rahotanni da ga birnin Sao Paulo na kasar Brazil na cewa wasu ma'aikatan gini na kamfanin Odebrecht sun rasa rayukan su, a ranar Larabar da ta gabata, bayan da wani sashe na rufin filin wasan Itaquerao ya fado musu.

Sashen rufin filin wasan na Itaquerao, ya sabbaba hallakar mutanen Biyu ne, yayin da suke kokarin kammala aikin wasu sassan sa. An ce dai a cikin wannan filin wasa na Itaquerao ne za a gudanar da wasu manyan wasanni na gasar cin kofin duniya dake tafe badi a kasar ta Brazil, ciki hadda wasannin bude gasar, da wasan kusa da na karshe.

Wannan hadari da a cewar kamfanin dake gudanar da aikin sashen karshe na rufin filin wasan, ya auku ne bayan da kugiyar dake rike da wani sashe na rufin filin wasan ta karye, wanda hakan ya sanya sashen rufin da ma ita kanta kugiyar fadowa, tare da hallaka wani ma'aikaci daya, da kuma direban motar dake sarrafa kugiyar. Kawo yanzu dai ba a tabbatar da ko rubzawar rufin filin wasan za ta shafi matsayin ginin filin baki daya ba.

Tuni dai ofishin mai gabatar da kara na birnin sao Paulo ya tabbatar da cewa, za a gudanar da cikakken bincike kan musabbabin aukuwar hadarin. A baya dai an sanya watan Disambar ya zamo wa'adi na karshe da aka baiwa kamfanin dake aikin wannan fili ya kammala dukkanin aikin sa, wanda tuni ya ce ya riga ya kammala kaso 94 bisa dari na daukacin aikin da yake gudanarwa.

A wani bangaren kuma shugaban hukumar gudanar da wasannin kwallo ta duniya FIFA Mr. Sepp Blatter, ya bayyana bakin cikin sa da faruwar wannan hadari, ya kuma mika sakwanin ta'aziyyar sa ga iyalan ma'aikatan da suka rasu. Shi ma kulaf din Corinthians, wanda ke mallakar sabon filin wasa, tuni ya mika na shi sakon ta'aziyar, tare da umarnin yin zaman jimami na kwanaki 7.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China