in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu
2013-12-06 17:52:21 cri

A kwai tukwicin sama da dala miliyan 400 ga 'yan wasan kasar Jamus, muddin suka dauko kofin duniya. 

Daga Najeriya sai kuma Jamus, inda hukumar kwallon kafar kasar ta bayyana aniyar ta, ta bada kyautar zinzurutun kudi da ya kai dalar Amurka 408,300, ga kowane dan wasan kungiyar kwallon kafar kasar, muddin dai kulaf din kasar ya samu nasarar lashe gasar kwallon kafa ta duniya dake tafe badi a kasar Brazil.

Kaftin din kulaf din kasar Philipp Lahm da ragowar 'yan wasan kulaf din sun amince da wannan kuduri, na tsayawa kan wannan adadi, wanda ya yi daidai da wanda aka sanyawa kungiyar yayin gasar cin kofin turai da ya gabata a kasashen Poland da Ukraine.

'Yan wasan dai sun fara samun kyautar kudi ne bayan da suka tsallaka zagayen waccan gasa na Biyu, inda aka baiwa kowannen su dalar Amurka 68,000 sakamakon kaiwar su ga matsayin quarterfinals, sai kuma dala 136,000 kowannen su bayan kaiwar su ga wasan kusa da na karshe, suka kuma samu kyautar dala 204,000 sakamakon kaiwa da suka yi zuwa wasan karshe na gasar.

Mai yiwuwa ne shugaban kamfanin Wanda na kasar Sin ya zuba jari ga kulaf din Rome.

Wasu rahotanni da kamfanonin watsa labaru na kasar Italiya suka bayar, na cewa, watakila shugaban kamfanin Wanda Wang Jianlin dake birnin Dalian na kasar Sin, ya zuba jari ga kulaf din Roma na kasar Italiya, koda yake ba a kai ga tabbatar da wannan labari ba ya zuwa yanzu.

Labaran da ke fita daga kafofin watsa labaru na cewa, mai yuwuwa ne akwai wani dan kasuwar kasar Sin da ke da niyar zuba jari ga kungiyar ta Rome, wanda ya kasance mafi arziki a kasar ta Sin, kuma shugaban kamfanin Wanda na birnin Dalian a kasar Sin Wang Jianlin. A halin yanzu, kamfanin Neep Roma Holding shi ke da ikon mallakar kaso 78 cikin dari na hanayen jarin kulaf din na Rome.

Cikin labarun da kafofin watsa labarun na kasar Italiya suka bayar don gane da hakan, sun yi sharhi kan Mr. Wang Jianlin, tare da gabatar da hotunansa a cikin labarinsu. Koda yake basu tabbatar da hakikanin gaskiyar labarin ba.

A gasar Serie A ta Italiya a wannan karo, ya zuwa yanzu, kungiyar Rome ta samu nasarar lashe wasannin ta 10, ta kuma yi kunnen doki sau 2, matakin da ya sanyata samun maki 32 da kasancewa a matsayi na farko a yanzu. Ta na kuma daya daga kungiyoyin kasar mafiya karfi da ake zatawa daukar kofin zakarun kasar a bana.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China