in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala zagayen farko na neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a Turai, da nahiyar kudancin Amurka, da nahiyar tsakiya da arewacin Amurka da kuma yankin Caribbean
2013-10-25 15:56:11 cri


Turai:

A ranar 16 ga watan nan da muke ciki ne aka kammala zagayen farko na gasannin rukuni-rukuni, na nahiyar Turai, tsakanin kasashen dake neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a buga badi a kasar Brazil.

Kungiyoyi 9 da suka shiga matsayin farko a rukuninsu sun samu damar shiga gasar cin kofin duniya na kasar Brazil kai tsaye, kuma kungiyoyi 8 da ke kan gaba a cikin kungiyoyi 9 wadanda suka kasance a matsayi na biyu a rukunin za su shiga zagaye na biyu.

Kafin wasan karshe a gasannin rukuni rukuni, akwai kungiyoyi biyar da suka riga suka tabbatar da kasancewar su a matsayin farko a rukunin nasu, wadannan kasashe sun hada da Italiya, da Netherlands, da Jamus, da Switzerland da kuma Belgium. A wasan karshe, sauran kungiyoyi biyu da suke kan gaba, wato Ingila da Spaniya, sun cimma nasarar kasancewa a matsayin farko a rukuninsu. Ingila ta lashe Poland da ci biyu da nema, yayin da ita kuma Spaniya ta lashe Georgia da ci biyu ba ko daya.

Ban da wadan nan kasashe, Rasha da Azerbaijan sun yi kunnen doki da ci daya da daya, wanda hakan ya sanya Rasha tabbata a matsayin farko a rukunin ta. Ko da yake Portugal ta doke Luxembourg da ci uku da nema a wannan rukuni, duk da haka akwai sauran maki daya a tsakaninta da Rasha, don haka Portugal ta zama a matsayi na biyu, inda da ta shiga zagayen gasar na biyu.

A rukunin G, kafin wasan karshe, Bosnia Helzegovina, da Girka sun samu maki daya, amma Bosnia Helzegovina ta fi Girka yawan kwallaye. A wasan ta na karshe Girka ta lashe Liechtenstein da ci biyu da nema, yayin da ita kuma Bosnia ta ci kwallo daya tak a minti na 70, wanda ya bata damar tabbata a matsayin farko a rukunin na ta.

Wannan ne karo na farko da Bosnia and Helzegovina ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya a tarihi. Yayin da Girka ta zama a matsayi na biyu, za kuma ta shiga zagayen gasar na biyu, a yunkurin ta na samun damar shiga gasar cin kofin duniyar dake tafe.

Don gane da sauran kasashe dake fafatawa wajen neman shiga gasar cin kofin duniyar kuwa, kasar Iceland na cikin kasashen da suka fi jawo hankalin ragowar kasashe, dama masu sha'awar kallon kwallon kafa. Kasar Iceland dai na da mutane kimanin dubu 320 ne kacal, amma a yanzu haka kungiyar kwallon kafar kasar ta shiga zagaye na biyu, na neman shiga gasar cin kofin duniyar dake tafe a badi. A wasan ta na karshe, Iceland ta yi kunnen doki da Norway da ci daya da daya, wanda hakan ya bata damar zama a matsayi na biyu a rukuninta, za kuma ta shiga zagayen gasar na biyu. Wannan ne dai sakamako mafi kyau da kasar ta Iceland ta taba samu a tarihin kwallon kafar ta.

Bisa kididdiga kasar Iceland na mataki na 126 ne a jerin kulaflikan kasashen dake taka leda a duniya, yayin da kuma a rukuninta, a zagayen farko na gasannin rukuni rukuni na nahiyar Turai da aka buga don neman shiga gasar cin kofin duniya dake tafe, take a matsayi na karshe. A wannan karo bayan kammala zagayen farko na gasar fidda gwani, Switzerland ta zama a matsayi na farko a rukunin, inda ita kuma Iceland ta zama na biyu, bayan ta lashe wasanni 5, ta kuma yi kunnen doki 2, cikin wasanni 10 na zagayen farko. Iceland din ta lashe Slovenia, da Norway da kuma Albania. Matakin da ya bata damar shiga zagaye na biyu, na neman shiga gasar cin kofin duniya a wannan karo. Kana matsayinta a jerin kulaflikan duniya ya daga zuwa 54.

Kamar yadda muka ambata al'ummar Iceland basu wuce mutum dubu 320 ba, don haka abu ne mai wahala a zaci wucewar kulaf din ta zuwa zagaye na biyu a nahiyar Turai, duba da cewa akwai manyan kungiyoyi mafiya karfi da kwarewa a nahiyar. Don haka, bayan da aka kammala zagayen farko na gasannin rukuni rukuni, dan wasan kungiyar kasar Iceland Kolbeinn Sigthorsson ya bayyana cewa, 'yan wasa dake kungiyarsa matasa ne dake da burin taka rawar gani a wannan karo, musamman zuwa zagayen gasar na biyu, yace yanzu haka kuma burin su ya cika. Sigthorsson ya ce yanzu haka suna cike da murnar shiga zagaye na biyu, suna kuma fatan buga wasannin gaba da kuma samun kyakkyawan sakamako.

Ban da wannan, sauran gasanni na wasannin karshe a zagayen farko sun kayatar matuka. Ga misali kasar Netherlands ta lashe Turkiya da ci biyu da nema, matakin da ya taimakawa Romania, ta shige gaban Turkiya tare da kasancewa a matsayi na biyu a rukunin. Sai kuma kasar Jamus wadda ta lashe Sweden da ci biyar da uku. Sa'an nan kuma Italiya da Armenia suka tashi kunnen doki da ci biyu da biyu.

Ya zuwa yanzu, an kammala zagayen farko na gasanni rukuni rukuni na nahiyar Turai, wadda aka buga domin share fagen shiga gasar cin kofin duniya mai zuwa, kuma kungiyoyi 9 da suka zama a matsayin farko a rukunin su, na rike da tikitin shiga gasar cin kofin duniyar kai tsaye. Wadannan kungiyoyi su ne Spaniya, da Ingila, da Rasha, da Italiya, da Netherlands. Ragowar sune Jamus, da Bosnia and Helzegovina, da Belgium da kuma Switzerland. Kana kungiyoyi 8 dake kan gaba a cikin kungiyoyi 9 dake matsayi na biyu a rukunin, za su shiga zagayen biyu, ciki hadda Croatia, da Portugal, da Girka, da Sweden, da Faransa, Ukraine, da Romania da kuma Iceland. Wadannan sune kungiyoyi 8 za su buga wasannin da za su fidda kungiyoyi 4, da zasu cike guraben kulaflikan da zasu Brazil domin halartar gasar cin kofin duniya dake tafe a shekarar 2014.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China