in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane Biyu sun halaka bayan da rufin filin wasan na Itaquerao ya fada musu
2013-12-06 17:52:21 cri

An yi alkawarin biyan Keshi dukkanin hakkokin sa.

To yanzu kuma sai Najeriya, inda mahukuntan kasar suka alkawarta biyan kocin Super Eagle Stephen Keshi, da mataimakin sa bashin hakkokin su da suke bi, da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 4.85.

Ma'aikatar wasannin kasar ce ta tabbatar da hakan a ranar juma'a 29 ga watan da ya gabata kamar yadda ministan wasannin kasar ya bayyana. Keshi, wanda ke bin bashin hakkokin sa tsawon watanni 5 da suka gabata ya jagoranci kulaf din na Super Eagle, wajen daukar kofin nahiyar Afirka da ya gabata, tare da samun nasarar shiga jerin kasashen da za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya dake tafe a badi.

Duk dai da irin nasarorin da kulaf din ke samu, a hannu guda jadawalin da hukumar FIFA ta fitar a baya bayan nan na nuna cewa yanzu haka Najeriyar ta sauko daga matsayi na 33 zuwa na 36 a fannin kulaflika mafiya kwarewa a duniya. Don gane da hakan Keshi ya ce sam hakan bai dame shi ba, kuma babu wata kasa da za ta tsorata shi, a kokarin da zai yi shi da 'yan wasan na Super Eagles na lashe kofin na duniya.

Rahotanni dai na nuna cewa kulaf din na Super Eagles dake dogaro kaco kan, ga kudaden da gwamnatin kasar ke samar ma sa, in banda dan abin da ba a rasa daga wasu kafofi ba, na fuskantar kalubalen kudin gudanarwa a 'yan shekarun nan. An dai ce akwai korafe korafe dake nuna cewa kudaden da kulaf din ke samu ba sa isa wajen sauke bukatun dake wuyansa.

1 2 3 4 5
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China