in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta shiga jerin kasashen da zasu taka leda a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a badi
2013-11-21 20:30:32 cri


Najeriya ta shiga jerin kasashen da zasu taka leda a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a yi a badi.

Babban kulaf din kwallon kafar tarayyar Najeriya wato Super Eagles, ya lallasa takwaransa na kasar Habasha da ci 2 da 1, yayin wasan zagaye na biyu, na share fagen shiga gasar cin kofin duniya da za fara badi a kasar Brazil.

Wasan na ranar Asabar din da ta gabata, wanda aka buga a garin Calabar, babban birnin jihar Cross River ya kayatar matuka. Kuma wannan ne karo na biyu, da kungiyar kasar Habashan ta sha kasha hannun Super Eagles cikin wannan wasanni na fidda gwani, bayan da a zagayan farko, kulaf din na Najeriya ya tashi wasan sa da Habashan a zagayen farko da ci 4 da 1.

Yayin wasan na ranar Asabar, dan wasan Najeriya Victor Moses ne ya fara jefa kwallo ta farko cikin minti na 20, ta bugun daga kai sai mai tsaron gida da Najeriyar ta samu, sakamakon taba kwallo da hannu da dan wasan Habasha ya yi. Sai kuma kwallo ta Biyu daga Victor Obinna cikin minti na 82.

Kasar Kwadebuwa ta tsallaka rukunin gasar cin kofin duniya dake tafe.

Baya ga Najeriya, ita ma kasar Kwadebuwa ta samu tsallake shingen shiga gasar cin kofin na duniya dake tafe a badi a karo na Uku a jere, bayan ta tashi kunnen doki da kasar Senegal da ci daya da daya a ranar Asabar. Tun da farko dai Senegal ce ta fara jefa kwallo a zaren Kwadebuwa ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da alkalin wasan ya kama Didier Drogba, da laifin yiwa Moussa Sow keta.

Daga bisani ana daf da tashi, dan wasan Kwadebuwa Salomon Kalou ya farke kwallon da aka jefa musu. Tarihi dai ya nuna cewa, kulaf din kasar ta Kwadebuwa bai taba samun damar wuce rukunin da yake ciki ba, a wassnin da yake bugawa cikin gasar cin kofin na duniya da yake halarta tun daga 2006 kawo wannan lokaci.
An sayar da dukkan tikitin kallon gasar cin kofin duniya ta Brazil a mataki na biyu cikin awoyi 7.

Rahotannin da muka samu sun bayyana cewa tuni aka fara sayar da tikitin kallon gasar cin kofin duniya da za a yi badi a kasar Brazil a matakin farko, inda yanzu haka aka kammala sayar da dukkan tikiti kimanin dubu 230, a mataki na biyu ta kafar yanar gizo na hukumar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA a cikin awoyi 7.

Hukumar FIFA ta bayyana cewa, kashi 62 cikin kashi dari, na yawan masu sayen tikitin 'yan kasar Brazilne. Ragowar kuwa sun fada ne hannayen 'yan sauran kasashen duniya, da yawan su suka fito daga kasashen Amurka, da Australia, da Ingila da kuma Argentina.

Har ila yau FIFA ta tabbatar da cewa za a fara sayar da tikitin kallon gasar a mataki na uku tun daga ranar 8 ga watan Disamba mai zuwa.

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China