in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kayatar da baki sosai kan harkokin zuba jari ga kasashen waje kai tsaye da kasar Sin ta yi
2013-07-19 16:54:46 cri
Bisa kididdigar da gwamnatin Sin ta yi kwanan baya, an ce, cikin farkon rabin shekarar bana, yawan jarin da Sin ta zuba kai tsaye ya kai dallar Amurka biliyan 45.6, inda ya nuna cewa adadin ya karu da kashi 29 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarar bara.

Dangane da wannan lamarin, masu ra'ayin kasa da kasa da wasu masana sun nuna cewa, halin da ake ciki yanzu na koma bayan tattalin arzikin duniya, kasar Sin ta kara saurin zuba jari ga kasashen waje, inda hakan na da muhimmanci ga kyautata yanayin tattalin arzikin duniya.

A cikin shafin tattalin arziki na jaridar Le Figaro ta kasar Faransa, an bada rahoton cewa, kasar Sin ta kara saurin sayen kamfanonin kasashen waje, musamman ma wasu kamfanoni masu harkar fasaha da kuma masu inganci a kasashen Turai.

Rahoton ya kuma kara da cewa, a halin yanzu, kamfanonin Sin na samun karbuwa sosai a kasuwar Turai, kuma za su ci gaba da bunkasa a kasuwar Turai cikin 'yan shekaru masu zuwa.

Farfesa Jean-Paul Larcon na kwalejin ilmin cinikayya ta birnin Paris na ganin cewa, bunkasuwar kamfanonin Sin a kasa da kasa, wani sakamako ne na manufar bude kofa ga waje, da kuma saurin ci gaban tattalin arziki da cinikayyar Sin.

To amma kasar Sin ta gamu da kalubaloli da dama wajen shigar da kamfanoninta zuwa kasa da kasa, a fuskoki kamar na koyon fasahohin zamani, kyautata fasahar sayar da hajoji da kama kafuwar tambarin kamfani ko masana'anta a duk duniya, sannan kuma ya kamata kamfanonin kasar Sin su rika samun matsayi mai rinjaye wajen yin takara.

Shafin intanet na Forbes, na kasar Amurka ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na ba da goyon baya ga kamfanonin kasar da suke zuwa kasashen waje da kuma ba da horaswa ga ma'aikatan kamfanonin. Gwamnatocin yankunan kasar Amurka na son samun jari daga kasar Sin, har ma wasu gwamnoni da magajin gari sun taba zuwa kasar Sin don neman jari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China