in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Ghana tana zawarcin masu zuba jari a fannin mai
2013-03-20 10:29:43 cri

Wani babban jami'in kasar Ghana ya bayyana ranar Talata cewa, kasar na zawarcin masu zuba jari da su zo su ci moriyar kyakyawan yanayi a kasar ta yammacin Afirka ta hanyar zuba jari a fannin albarkatun mai da iskar gas.

Ministan makamashi da man fetur Emmanuel Armah Kofi Buah ne ya yi wannan kira yayin da ya bude taron binciko albarkatun man fetur da gas jiko na 17.

Ya ce, ma'aikatar tasa da ma sauran cibiyoyi dake karkashinta wato hukumar man fetur, da hukumar albarkatun mai ta kasar Ghana (GNPC) na masu yin maraba da kamfanoni masu harkar mai na kasa da kasa (IOC) zuwa kasar Ghana ganin cewa, suna da buri guda na bincikowa da kuma sarrafa mai ta hanya da ta dace da kiyaye muhalli.

Ministan ya ce, kasar ta yammacin Afirka wacce ta fara sarrafa mai a shekarar 2010 tana da kyakyawan yanayi na siyasa da muhallin harkar kudade, ga masu zuba jari a masana'antar mai da gas.

Ya ci gaba da cewa, na kafa kyakyawan tubali na inganta rayuwa ta hanyar bunkasar tattalin arziki, haraji da suka dace, da ma tsarin doka da kuma manufofi na kudade, inda ya kara da cewa, zuba jarin zai amfani jama'ar kasar Ghana da masu zuba jarin kansu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China