Kakakin ma'aikatar cinikayya ta Sin, Shen Danyang wanda ya bayyana kiyasin a gun taron manema labaru da aka shirya a nan birnin Beijing yace Sin za ta samu jari daga kasashen ketare cikin dorewa a bana.
Game da zuba jari a kasashen ketare kuma, daga watan Janairu zuwa Mayu na bana, masu zuba jari na Sin sun zuba jari kai tsaye ga kamfanoni 2,494 na kasashe da yankuna 144 na duniya, yawan kudin ya kai dala biliyan 34.3, wanda ya karu da kashi 20 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara.
Ban da haka, Mr Shen ya kara da cewa, lokacin da yawan kudin da Sin ta zuba a kasashen ketare kai tsaye ke karuwa cikin sauri, sassan da batun ya shafa su ma sun karu sosai. A farkon watanni biyar na bana, kimanin kashi 90 cikin dari na jarin da kamfanonin Sin suka zuba a kasashen ketare ya shafi sana'ar ba da hidimomi, kasuwannin sari da kananan ciniki, gine-gine, sana'ar kera, da kuma hakar ma'adinai.(Fatima)