Shugaban sashen kula da harkokin zuba jari da kamfanoni na hukumar cinikayya da bunkasuwa ta MDD, Mr. Zhan Xiaoning ya bayyana cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen zubar da karin jarin kai tsaye ga kasashen wajen. Cikin shekarar 2012, gaba daya jarin da kasar Sin ta zuba ga kasashen waje kai tsaya ya kai dallar Amurka biliyan 84, wanda ya sa Sin ta kasance kasa ta uku wajen zuba jari ga kasashen wajen, bayan kasar Amurka da ta Japan. Bugu da kari, bisa binciken da aka yi game da yanayin zuba jari ga kasashen waje, an ce, kasar Sin ta fi samun ci gaba kan wannan fannin.
Kuma kan fannin samun jari daga kasashen wajen, an ce, a halin yanzu, kasar Sin ta fi samun jari daga kasashen ketare cikin duk kasashe masu tasowa, inda jarin da ta samu ya kai dallar Amurka biliyan 121, shi ya sa, kasar Sin ta kasance kasa mafi jawo hankulan manyan kamfanonin ketare wajen zuba jari. (Maryam)