in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kasuwar kasar Sin na burin habaka harkokin zuba jari a Afirka
2013-08-21 10:34:58 cri

Kungiyar 'yan kasuwar kasar Sin ta bayyana muhimmancin da kungiyar kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki ta BRICS ke da shi, wajen habaka harkokin zuba jari a nahiyar Afirka.

Mukaddashin shugaban kungiyar Zehua Ma ne ya bayyana hakan a ranar Talata 20 ga wata a birnin Johannesburg na Afrika ta Kudu, yayin da yake jawabi gaban mahalarta taron kungiyoyin 'yan kasuwar kasashe mambobin kungiyar ta BRICS. Ma, ya kara da cewa, burin kungiyarsa ne ta ga ta taimakawa nahiyar Afirka, da hanyoyin magance karancin ayyukan yi da fatara, ta hanyar samar da karin kudaden zuba jari a nahiyar.

Har ila yau, mukaddashin kungiyar 'yan kasuwar kasar ta Sin, ya ce, Sin da Afirka, na da bukatar juna a fagen samar da ci gaba ta fuskar cinikayya da bunkasar tattalin arziki, don haka, za su dauki dukkanin matakan da suka wajaba, wajen ganin an cimma wannan buri.

Taron na yini biyu wanda ya samu halartar jagororin kungiyoyin 'yan kasuwa daga kasashe mambobin kungiyar BRICS, daga kasashen Brazil, da Rasha, da Indiya, da Sin da kuma kasar Afirka ta Kudu, ya mai da hankali ne ga tattauna batutuwan da suka shafi habaka hadin gwiwar cinikayya, domin ci gaban nahiyar Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China