Firimiyan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira da a dauki karin matakan da suka dace, domin habaka tattalin arziki, da bunkasa rayuwar jama'a.
Li wanda ya bayyana hakan a ranar Talatar da ta gabata, yayin da yake jawabi gaban mahalarta wani taron manyan jami'an gwamnati a lardin Heilongjiang, dake arewa maso gabashin kasar Sin, ya kara da cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da bunkasa sannu a hankali, sakamakon matakan da ake dauka tsahon lokaci. Wadannan matakai, a cewarsa, sun hada da tabbatar da gudanar ayyukan hukuma a dukkanin matakan jagoranci, da samar da ayyukan yi, daidaita farashin kayayyaki tare da bunkasa birane.
Firimiyan kasar ta Sin ya bayyana ci gaba a matsayin babban ginshikin warware matsalolin kasa, yana mai tabbatar da ci gaba da daukar matakan karfafa hakan ta hanyoyin kimiyya, da inganta ayyuka, kiwon lafiya da kuma bunkasa rayuwar jama'a daga dukkanin fannoni.
Taron manyan jami'an dai ya samu halartar jagorori daga lardunan Heilongjiang, da Liaoning, da Jilin, da Fujian, da Henan da kuma yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kansa. An kuma gudanar da wannan taro gabanin cikakken zama na 3, na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwamins ta Sin karo 18, wanda za a fara a ranar Asabar mai zuwa. (Saminu)