A ran 14 ga wata a babban dakin taron jama'a da ke birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da wakilan kasashen waje da suka halarci taron shekara-shekara na 2013 na kwamitin hadin kan kasashen duniya don kare muhalli da raya kasar Sin, inda suka tattauna.
Li Keqiang ya yi maraba da wakilan da suka zo kasar Sin don halartar taron, kuma ya yaba mausu da mai da hankali da goyon bayan da suka nuna a kan sha'anonin kare muhalli da bunkasuwa a kasar Sin, yana mai cewa, shawarar da suka bayar ga kasar Sin yana da amfaninsu, kuma mai yakini ne.
Mr. Li ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai wajen samun daidaito a tsakanin raya kasa da kare muhalli, don haka za a gaba da kara kare muhalli a yayin da take sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki.
Haka kuma firaministan ya kara da cewa, kasar Sin tana son inganta hadin kai da sauran kasashen duniya, ba ma kawai a fannin mu'ammalar ra'ayoyi ba, har ma da kara hadin kai a fannonin fasaha da masana'antu, don ciyar da kafa al'adun halittu tare. A karshe, ya yi fatan walikan za su kara ba da shawara mai kyau ga al'amuran kare muhalli da raya kasar Sin.(Danladi)