in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang da shugabannin kungiyar EU sun bayyanawa 'yan jarida sakamakon ganawarsu
2013-11-21 21:02:54 cri
Yau Alhamis 21 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar dokokin Turai Herman Von Rompuy da kuma shugaban kwamitin kungiyar EU Manuel Durao Barroso sun gana da 'yan jarida tare, inda suka bayyana sakamakon da aka samu a gun taron ganawa a tsakanin shugabannin Sin da kungiyar EU karo na 16.

Shugabannin sun cimma daidaito a fannoni biyar. Na farko shi ne gabatar da shirin hadin gwiwar Sin da Turai na shekarar 2020. Na biyu, sun sanar da kaddamar da tattaunawa game da zuba jari a tsakaninsu a hukumance. Na uku, za su tattauna kan kafa yankin yin ciniki cikin 'yanci. Na hudu, za su kara yin mu'amala a fannin al'adu. Kuma na biyar, za su kara yin hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa da shiyya-shiyya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China