A cikin jawabinsa, Le Keqiang ya ba da shawarar kara hadin gwiwa wajen tinkarar kalubaloli tare. Ya kuma bayyana bukatar sanya kulawa ga manufar bunkasa, da ta hada da batun ingancin hatsi da na makamashi, da kariya daga bala'u daga Indallahi, da batun sauyin yanayi, kiwon lafiya da sauran muhimman batutuwa.
Ban da haka, Le Keqiang ya ba da shawarar kafa wani tsarin tsaro da zai dace da halin da ake ciki a wannan yanki, tare da biyan bukatun da ake yi daga fannoni daban-daban.
Haka zalika, Li Keqiang ya bayyana matsayin kasar Sin kan batun tekun Kudu, yana mai cewa, Sin za ta yi kokari tare da kasahen ASEAN, wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin tekun Kudu, da aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya, tare da kaddamar da ka'idar tekun bisa matsayar da suka cimma.
A hannu guda kuma, shugabannin kasashen ASEAN na fatan daidaita batun tekun Kudu cikin lumana, tare kuma da yin hadin kai wajen tabbatar da zaman lafiya da karko, da ma wadatar yankin. (Amina)