A gun taron ganawa a tsakanin shugabannin Sin da kungiyar EU karo na 16 da aka gudanar a wannan mako a nan birnin Beijing, an gabatar da shirin hadin gwiwar Sin da Turai na shekarar 2020, kana an sanar da kaddamar da tattaunawa game da zuba jari a tsakaninsu a hukumance, da kuma gabatar da burin kara yawan cinikayya a tsakanin Sin da Turai a shekarar 2020 da zai kai dala biliyan 1000. A ganin Li Keqiang, wannan zai kara bada dama ga Sin da kasashen Turai ciki har da kasar Ingila a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya.
Sharhin ya ce, muddin ana son a fuskanci kalubale wajen farfado da tattalin arzikin duniya, kamata ya yi Sin da Turai su kara yin hadin gwiwa da taimakawa juna, kana su yi kokarin warware matsalolinsu da kansu.
A shekarar bana, Sin ta fuskanci mawuyacin hali a ciki da waje, kana tana gamuwa da matsin lamba na raguwar tattalin arziki. Game da wannan, Li Keqiang ya nuna cewa, Sin ta gabatar da wasu matakai don sa kaimi ga samun bunkasuwar tattalin arziki, da kuma fadada bukatunta na cikin gida ta hanyar kyautata tsarinta.
Ban da wannan kuma, sharhin ya ce, kokarin Sin na tafiya da zamani zai samar da kyakkyawar dama ga Sin da kasashen Turai ciki har da kasar Ingila wajen inganta hadin gwiwarsu ta samun moriyar juna. (Zainab)