Da yake jawabi gaban mahalarta taron, firaminista Li Keqiang ya nuna cewa, a 'yan watanni na farkon shekarar bana, Sin ta fuskanci kalubalen koma bayan tattalin arziki, wanda hakan ya jawo wahala ga gwamnatin tsakiya wajen samun karin kudaden shiga. A cikin wannan yanayi ne, gwamnatin kasar ta Sin ta dauki sabon matakan daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan fannoni, kuma an samu sakamako na a zo a gani. A cewarsa, ya zuwa yanzu Sin ta samu bunkasuwar tattalin arzikin yadda ya kamata, tare da kiyasin samun bunkasuwar kasuwanni.
Li keqiang ya kara da cewa, aikin duba sha'anin kudi na da muhimmanci sosai wajen sa kaimi ga ayyukan kudi, da ma daidaita harkokin bunkasa kasa. Don haka ne hukumomi a wannan fanni su kara sa ido kan wannan fanni na kiyaye dukiyar al'umma, da kadarorin kasar, da hakkin jami'ai a fannin tattalin arziki, su kuma gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ban da haka Li keqiang, ya bayyana bukatar daukar matakan kara karfin sarrafa, tare da rigakafin aukuwar hadarori. Dadin dadawa, ya ce basussukan da gwamnatin kasar ta samar suna cikin tsarin nagarta. Haka zalika, ya gabatar da shawarwari uku dangane da ayyukan duba sha'anin kudi bisa halin da Sin ke ciki.
Da farko tabbatar da tsaron kudin kasar, sai yaki da cin hanci da rashawa, da kuma ba da taimako wajen yin hadin kai tsakanin kasa da kasa.
An ce, mambobin kungiyar duba sha'anin kudi da masu sa ido sama da 680 daga kasashe fiye da 160 ne suka halarci bikin bude taron. (Amina)