A gun taron, an bayyana cewa, yayin taron cikakken zama na 3 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, an tsara shirin karfafa aikin yin gyare-gyare daga dukkan fannoni zuwa wani lokaci a nan gaba. Wajibi ne hukumomi na matakai daban daban su bi manufar da aka cimma a yayin taron, da daukar hakikanin matakai, don kara aiwatar da gyare-gyare, da sa kaimi ga raya tattalin arziki yadda ya kamata, ta yadda jama'ar kasar za su kara ci moriyar sakamakon gyare-gyare da raya kasa da aka samu.
A gun taron, an bayyana cewa, domin kara aiwatar da gyare-gyare, dole ne a cika alkawarin da aka dauka wajen inganta aikin yin gyare-gyare da karfafa zukatan jama'a game da aikin yin gyare-gyare, don aza wani harsashi wajen gudanar da wannan aiki, da duba yadda aka aiwatar da manufar, ta yadda za a kara himma wajen aiwatar da gyare-gyare daga fannoni daban-daban, kuma a samu sakamakon gyare-gyaren a kai a kai.(Bako)