Yau Alhamis 21 ga wata a nan birnin Beijing, firaministan kasar Sin Li Keqiang da shugaban majalisar dokokin Turai Herman Von Rompuy da kuma shugaban kwamitin kungiyar EU Manuel Durao Barroso suka shugabanci taron ganawa a tsakanin shugabannin Sin da kungiyar EU karo na 16, inda Li Keqiang ya nuna cewa, kungiyar EU muhimmin bangare ne a fadin duniya, kana muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ta kasar Sin yayin da kasar ke kokarin tafiyar da zamani. Sin ta dora muhimmanci sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Turai, kuma tana son yin kokari tare da kasashen Turai wajen inganta dangantakarsu ta abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
Kana Li Keqiang ya nuna cewa, Sin ta nuna goyon baya ga manyan kamfanonin kasar da su zuba jari a kasashen Turai, kuma tana fatan kasashen Turai za su sassauta kayyadewar fitar da kayayyakin fasahohin zamani zuwa kasar Sin. Kuma Sin tana fatan ita da kasashen Turai za su nuna adawa ga ra'ayin bada kariya ga cinikayya da zuba jari, da fadada hadin gwiwa da inganta shi. (Zainab)