A gun taron, an yi nuni da cewa, game da halin tattalin arziki mai sarkakkiya da ake ciki a gida da waje a bana, gwamnatin tsakiya ta Sin ta tsara manufofin raya tattalin arziki, da canja salon bunkasuwa, da sa kaimi ga yin kwaskwarima, da tabbatar da raya tattalin arziki yadda ya kamata. Bisa kididdigar da aka bayar, an ce, tattalin arziki na watan Yuni zuwa Satumba na kasar Sin ya samu bunkasuwa yadda ya kamata.
A gun taron, an yi nazari game da matsalolin da ake ciki wajen sa kaimi ga yin kwaskwarima da canja salon raya tattalin arziki. An nuna cewa, ya kamata a kara himma wajen karfafa aikin yin kwaskwarima da canja salon raya tattalin arziki, da ci gaba da gudanar da matakan da aka tsara, don kara samar da moriyar yin gyare-gyare ga jama'a, ta yadda za a kara gudanar da manufofi, da kyautata aikin raya tattalin arziki.(Bako)